waazi

Allahu Akbar Prof Muqari Yaraba Gardama Hujjoji 20 Cikin aayoyi Da Hadith Iyayen Annabi Ba Yan Wuta Bane Raddi Zuwaga Jalo Jalingo

Daya daga cikin fitattun malumai kuma masu tarin ilimi da ya yakasance ko bakabin aqidar da yake kai kasan cewa ya amsa sunansa na malami Sheick Ibrahim muqari said limamin babban masallacin nigeria.

ya bada Hujjoji abin gamsuwa gameda Zantuttunkan cewa wai iyayen annabi suna wuta waiyazubillahi kamar yadda shugaban majalisar malamai na izalatul bidia wa iqamatussunna nakasa ya ke daawa akai wanda har littafi yayi domin tabbatar da kudurinsa.

ga hujjojin prof. Ibrahim Muqari gameda wannan alamari.

*_IYAYEN ANNABI SAW MUSULMAI NE MASU KADAITA ALLAH, AKAN ADDININ ANNABI IBRAHIM AS.

1.Hujjar mu ta farko itace Addu’ar Annabi Ibrahim da Annabi Isma’il Alaihimas Salam a Suratul Baqara aya ta 128

رَبَّنا وَاجعَلنا مُسلِمَينِ لَكَ وَمِن ذُرِّيَّتِنا أُمَّةً مُسلِمَةً لَكَ وَأَرِنا مَناسِكَنا وَتُب عَلَينا ۖ إِنَّكَ أَنتَ التَّوّابُ الرَّحيمُ

“Ya Ubangijnmu! Ka sanyã mu, mu biyu, waɗanda suka sallama (al’amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al’umma mai sallamãwa zuwa gare Ka, Kuma Ka nũna mana wurãren ibãdar hajjinmu, kuma Ka karɓi tũba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tũba, Mai rahama.

Da kuma Suratu Ibrahim aya ta 37

رَبَّنا إِنّي أَسكَنتُ مِن ذُرِّيَّتي بِوادٍ غَيرِ ذي زَرعٍ عِندَ بَيتِكَ المُحَرَّمِ رَبَّنا لِيُقيمُوا الصَّلاةَ فَاجعَل أَفئِدَةً مِنَ النّاسِ تَهوي إِلَيهِم وَارزُقهُم مِنَ الثَّمَراتِ لَعَلَّهُم يَشكُرونَ

“Yã Ubangijinmu! Lalle ne ni, na zaunar da zuriyata ga rãfi wanda ba ma’abũcin shũka ba, a wurin ¦ãkinka mai alfarma. Yã Ubangijinmu! Dõmin su tsayar da salla. Sai Ka sanya zukãta daga mutãne sunã gaggãwar bẽgenzuwa gare su, kuma ka azurtã su daga ‘ya’yan itãce, mai yiwuwã ne sunã gõdẽwã.”

Kuma babu kokonto cewa Allah ya amsa ma Annabi Ibrahim da Annabi Isma’il Addu’ar su.
Kuma Addu’ar ce taita bin tsatson su har Annabi Muhammadu SAW ya bayyana.

*Ibn Munzari a Tafsirin sa ƙarƙashin aya ta 40 a suratu Ibrahim

رَبِّ اجعَلني مُقيمَ الصَّلاةِ وَمِن ذُرِّيَّتي ۚ رَبَّنا وَتَقَبَّل دُعاءِ

“Yã Ubangijina! Ka sanyã ni mai tsayar da salla. Kuma daga zũriyyata. Yã Ubangijinmu! Kuma Ka karɓi addu’ata.”

Ibn Munzari yace :

فلن يزل من ذرية ابراهيم اناس على الفطرة يعبدون الله تعالى.

Mutane a Zuri’ar Annabi Ibrahim basu gushe ba suna kan Addinin suna Bauta ma Allah.

*Ibn Jaririɗ Dabariy a tafsirin sa yace :

استجاب الله له وجعل البلد امنا، ورزق اهله من الثمرات وجعله امام ، وجعل من ذريته من يقيم الصلؤة.

Allah ya amsa masa Addu’ar sa kuma ya sanya garin (Makkah) yazama Amintacce, kuma ya azurta mutanan garin da yayan itatuwa kuma ya sanya shi jagora, kuma ya sanya Masu tsaida Sallah daga cikin zuri’ar sa.

  1. Abu Nu’aim ya ruwaici Hadisi

عن ابن عباس رضي الله عنهما : ان رسول الله صلى الله عليه وسلم قال : لم ياتق ابوي قط على سفاح ، لم يزل الله ينقلني من الاصلاب اليبة الى الارحام الطاهراة مصفى مهذبا لا تتشعب شعبتان الا كنت في خيرهما.

Daga Sayyidina Abbas RTA yace : Manzon Allah SAW yace : Iyayena basu taba fadawa cikin wata barna ba, Allah bai gushe ba yana ciratar dani daga Tsatso mai tsarki zuwa Mahaifa mai Tsarki, Abar ysarkakewa da tantancewa, wani bangare basu taba rabuwa biyu ba face sai na kasance cikin mafi Alkhairin su.

*Ibn Hajar Alhaitamiy a sharhin dayayi ma Hamziyya, a shafi na 29 qarqashin baitin da Imam Busiriy yakecewa :

لم تزل في ضماءر الكون تختار ** لك الامهات ولاباء
Ya Rasulullah SAW baka gushe ba acikin boyayyun tsatso Allah yana zabar maka uwaye da Iyaye maza.

Sai Alhaitamiy yace :

ان اباء النبي صلى الله عليه وسلم غير الانبياء وامهاته الى ادم وحواء ليس فيهم كافر.

Lallai iyayen Annabi SAW maza da mata gaba daya babu Kafiri acikin su tin daga kan Sayyiduna Abdullahi da Sayyadatuna Ameenah har zuwa Annabi Adam da Hauwa’u.

لان الكافر لا يقال فى حقه انه مختار وكريم ولا طاهر بل نجس كما في اية ( انما المشركون نخس).

Yacigaba da cewa: Domin ba’a cema kafiri Mai tsarki ko zababbe ko karimi saboda Ayar Alqur’ani na cikin suratut Tauba ;
Allah yace : (Lallai su Mushrikai Najasa ne.).

Lallai da ace acikin iyayen Annabi SAW akwai wanda ba musulmi ba, da Annabi SAW bazai fadi wancan hadisin ba.

Insha Allah zamu cigaba da kawo hujjoji a rubutu na gaba.

Allah ya qara ma Iyayen Annabi SAW daraja, dan tsarkin Ruhin Annabi Muhammadu SAW.

allah ya karawa iyyen annabi daraja amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button
WP2Social Auto Publish Powered By : XYZScripts.com