Bello Turji

Kalli yadda wasu manyan maluma 2 sun shaa da kyar wajen yaran bello turji

Malam Musa Lukuwa da Malam Murtala Assada sun tsalke rijiya da baya a harin ‘yan bindiga a karamar hukumar Gudu

Shahararrun Malaman addini biyu ‘yan asalin jihar Sokoto Sheikh Musa Ayuba Lukuwa da Sheikh Murtala Bello Assada sun tsalke rijiya da a wani hari da ‘yan bindiga su kai wa tawagar su a hanyar su ta dawo wa gida daga kasar Ghana a wajen yada addinin musulunci.

Malam Murtala Assada ya ce” Bayan mun fito kasar Nijar cikin kwanciyar hankali, mu na shigowa Najeriya a hanyar Balle zuwa Sokoto ne mu ka ci karo da ‘yan bindiga a tsakanin Balle da Tangaza”

“Matasa ne ‘yan kasa da shekaru 30, kowannen su dauke da bindiga kirar AK47, sun kai su 20”.

“Mu na ganin haka sai mu ka fadawa Malam Musa Lukuwa cewa barayi ne a gaban mu, sai Malam ya ce mu ci gaba da tafiya tare da ambaton Allah”.

“Haka mu ka ratsa a tsakanin su babu wanda ya ce mana uffan, su na kallon mu su na mamaki, har sai da mu ka wuce ne sai suka dauko mashuna su ka biyo mu, amman Allah bai ba su nasara akan mu ba”.

re

“Saboda haka mu na kira ga Gwamnati da ta daina yaudaran al’umma cewa an samu zaman lafiya, na rantse da Allah karya ce, babu wani zaman lafiya da aka samu”. Inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button
WP2Social Auto Publish Powered By : XYZScripts.com