Trending

Kalli Wannan Video Kafin Ka Tura Yayanka Makarantar Boarding

YA’DUWAR ZINA ACIKIN AL’UMMA
Acikin kashi na farko munyi magana akan illolin da ya’duwar zina take kawo ma al’ummah. Yanzu kuma in sha Allahu zamu duba muga wasu daga cikin dalilan da suka kawo wannan bala’i :

 1. TALLE : Mafiya yawan yara Matan dake yawon talle acikin kasuwanni, Garejoji, Tashoshin Mota, da Unguwanni, suna cikin hatsarin afkawa cikin wannan mummunar dabi’a. Ba don komai ba sai saboda yadda kullum zasu rika jin kalamai na batsa da Kuma Miyagun wasanni irin na batsa da suke samu daga Shashashun samari da kuma tsofaffin ‘Yan tasha.
 2. WAYOYIN SALULA : Wayoyin Salula suna taka mummunar rawa cikin yaduwar fasadi da lalacewar tarbiyyar al’ummah. Musamman ta bangaren Hotuna da Bidiyo na batsa da recording na kalmomin batsa wanda Matasa maza da Mata suke turawa a wayoyinsu.

 3. Yara Qanana sukan kalli Hotunan yadda ake jima’i. Daga nan kuma sai Shedanci ya shiga zukatansu su fara tunanin hanyoyin da zasu bi su rika samun biyan bukatarsu, alhali da chan irin wannan tunanin bai ta’ba shiga kwakwalwarsu ba.
 4. WHATSAPP : Ita ma kafar sadarwa ta whatsapp tana taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar al’ummah. Harma ta zarce Facebook ko Twitter.
  Domin kuwa a Whatsapp ne watsatsun Samari da ‘Yan Mata (har ma da wasu Matan auren) suke bude groups musamman don koyar da zina!!.

 5. Ta wannan hanyar suke sabawa da juna har su rika haduwa da juna. Akwai ma Kungiyoyin Matan aure ‘Yan Madigo wadanda har auren juna suke yi. (Wal Iyazu bil Lahi).
 6. MAKARANTUN SAKANDIRE : Akwai Yara Mata da dama wadanda sun lalace ne tun a Makarantun Sakandiren kwana (Boarding Schools) ta sanadiyyar Malamansu dake tursasa musu suyi Zina dasu, Ko kuma su atsakanin Junansu su rika aikata madigo
  Hakanan a bangaren Mazan ma wasu tun daga Sakandire suke zama ‘Yan Luwa’di ta hanyar yi da junansu ko da Malumansu.
 7. MANYAN MAKARANTU : Su ma wadannan sun zama manyan dalilan watsewa ga wasu ta dalilin chakuduwar jinsi (Maza da Mata awaje guda).

 8. Zaka ga har abota ake Qullawa atsakanin Mata da Maza. Sai kaga Matar aure ko Qatuwar Budurwa ta Qulla abota tsakaninta da wani Qato haka kawai saboda ajinsu guda.

 9. Hakanan munsha jin yadda wasu lalatattun lakcharori suke tursasa yara Mata wajen yin zina dasu saboda su basu Maki (Marks).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button
WP2Social Auto Publish Powered By : XYZScripts.com