Bello Turji

Yaran Bello Turji Sunfara Yin Shiga Mata Yayan Kai Hari A Zamfara Da Sokoto

Wani sabon faifan video ya bayyana inda yaran kasurgumin dan taaddan nan mai damfara da garkuwa da mutane gamida kisan kiyashiwa wanda basuji ba basu gani ba mai suna. bello turji sun sauya salon kai hari.

Asirin su sabon shirin nasu ya tonune inda suka kai hari a wasu kauyuka 2 a jahar Sokoto inda sukayi kokarin shigowa kauyukan a hankali sanye da hijjabai kafin saura su biyo bayansu domin sa ido ko jamian tsaro suna nan.

Wannan mataki da suka dauka ya biyo bayan jajircewar sojojin nigeria inda akayi nasarar fara basu manya manyan makamai kamar yadda yan taaddan suke dauke da muggan makamai.

sai dai ban bancin shine su sojojin nigeria sunada waye ta da horo ta musamman gameda dubar burun yaki shiyasa har yanzu yan taadan suke tsoron sojojin nigeria.

wannan salo da suka fito dashi sojojin nigeria sunyi hubba saa domin yunwurin dakile wannan sabon salon cutarwa da suka sake bullowa da shi domin kai muggan hare hare .

zuwa yanzu dai rahotanni dake da alaqa da abinda sukayi a kauyukan bai zoba tukun amma da zarar sabon lamari yazi zaku sani mungode da ziyarah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button
WP2Social Auto Publish Powered By : XYZScripts.com