Abinda Yasa Na Yanke Al Aurata Da Kaina Wani Matashi Nai Shekaru 44

Inda ranka zaka sha kallo wani abin mamaki wanda bamu taba tsammani ba ya faru da wani matashi dan kimanin shekaru 44 da haihuwa ya yanke azzakarinsa da kansa
Ya Yanke Al’aurarsa Domin Kawar Da Sha’awa Saboda Ya Samu Damar Bautawa Allah
Mutumin da ya datse al’aurarsa domin kawar da sha’awar jima’i a Benue, ya ce ya yi hakan ne domin mayar da hankali kan bautar Allah.
Terhemen Anongo, mai shekaru 44 da haihuwa mazaunin garin Gboko ne dake jihar Benue.
Anongo, wanda ya bar makarantar koyon aikin likitanci ta Jami’ar Ibadan bisa zargin rashin lafiya, ya ce ya yi hakan ne bisa imaninsa na addini cewa tun da bai yi aure ba, yana bukatar ya bauta wa Allah da aminci.
“Ina cikin koshin lafiya babu matsala, ina jira kawai lokacin da raunin zai warke don in cire ɗinkin. ” Inji shi.