mugyara mata

Shin Kunsan Yadda Ake Jimai da Mace Mi Ciki Da Amfanin Saduwa Da Ciki

Tambaya :

Malam na kan ji wasu mutane na fadar cewa ba ya halatta idan matar mutum tana da juna biyu ya yi jima’i da ita har sai ta haihu meye gaskiya maganar ????????

 

AMSA :

To dan’uwa ya halatta a sadu damace lokacin d take da ciki, saboda fadin Annabi tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi : “Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shaya da ruwansa ga shukar waninsa

” Abu-dawud : ayim yana cewa :”Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta ruwa” Tahzibussunan 1\193 .

Masana likitanci suna cewa: Ba’a so miji ya dinga hawa kan matarsa lokacin da take da ciki, zai fi kyau ta dinga yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda kwanciya akanta yana iya wahalar da yaron .

karin bayani gameda wannan al amari

Sannan yawanci mata ba su cika son yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a karanta saduwa a wadannan lokutan. Allah ne ma fi sani .

An shawarci mata su dinga kwanciyar kaikaice a lokacin da cikinsu ya kai wata shida, domin hakan zai taimaka wajen hana haihuwar da ba rai.

Wani nazari da aka yi a kan mata sama da 1,000 dubu daya ya gano cewa akwai karuwa hadari ga mace ta dinga kwanciya a rigingine yayin da cikinta ya shiga wata shida.

Nazarin ya yi duba ne a kan mata masu ciki 291 da suka haifi ‘ya’ya ba rai, da kuma mata 735 da suke haifar jariransu a raye.

Masu binciken sun ce yanayin kwanciyar da mata suke yi idan za su yi bacci shi ya fi matukar muhimmanci, kuma ka da su damu idan suka ga gansu a rigingine yayin da suka farka.

mahimmin abubuwa da yakamata ku sani gameda matta masu ciki

Kusan daya daga cikin mata masu ciki 225 a Birtaniya su kan haifi ‘ya’ya ba rai, kuma nazarin ya kididdige cewa kusan jarirai 130 za a ceto a shekara idan mata masu ciki suna kwanciya da gefe daya.

Ko tashi daga bacci a rigingine na da matsala?

Farfesa Alexander Heazell, darakta ne a cibiyar Tommy da ke nazari kan haifar yara ba rai a asibitin St Mary da ke Manchester, wanda kuma shi ne ya jagoranci binciken, na bai wa mata masu ciki shawara a kan su dinga kwanciya da gefe daya idan za su kwanta, ko da kuwa da rana ne.

“Abin da ba a so shi ne mata masu ciki su farka a rigingine kuma su yi tsammanin wani abu mara kyau ka iya samun jaririnsu.”

“Tambayar da muka yi ita ce, takamaimai wacce irin kwanciya mutane suke yi idan za su yi bacci, kuma shi ne abu mai muhimmanci idan mutum yana daukar lokaci mai tsawo a irin wannan kwanciyar fiye da yadda za ka yi a ko wanne bangare.

“Har ila yau kuma ba za ka iya yin wani abu game da yanayin da ka tashi ba, amma za ka iya yin wani abu game da yadda za ka kwanta bacci.”

Abubuwan da ya kamata ka yi idan zaka yi bacci

  • Ki saka filo daya ko sama da haka a gefen bayanki don ya taimaka maki yin bacci ta gefe daya
  • Idan kuma kin tashi cikin dare, ki duba yanayin kwanciyar taki sannan ki koma baccinki ta daya gefen
  • Kitabbatar da cewa a ko wanne lokaci za ki yi bacci to ki kwanta ta bangare maimakon rigingine, ko da rana ko da daddare
  • Idankin tashi a rigingine da daddare, kar ki damu kawai ki juya gefe daya ki ci gaba da baccinki
  • Sai dai nazarin bai gano wani bambaci tsakanin kwanciya a gefen dama ko a hagu ba

Masu binciken ba za su iya cewa komai game da dalilin da ya sa ake samun karuwar haifar yara ba rai ba, sai dai akwai wasu bayanai da dama da aka tattara da suke nuna cewa a lokacin da

mace mai ciki take kwanciya rigingine, nauyin jariri da na mahaifa na haduwa su takura jini inda hakan kuma kan haddasa wa jariri toshewar jinin da yake zagayawa da kuma iskar da yake samu.

sabon binciki mai mahimmanci gameda mata masu ciki

Edward Morris na BJOG ya ce, “Mun yi matukar maraba da samun wannan sabon bincike”.

“Wannan nazari ne mai matukar muhimmanci wanda zai kara tabbatarwa da jiki cewa yin bacci a ringine ga matan da cikinsu ya kai wata shida na sa su fuskanci barazanar haihuwar da ba rai,” in ji shi.

Cibiyar nazari ta Tommy ta gabatar da wani gangami da zai kara wayar wa da mata kai a kan binciken da kuma ba su kwarin gwiwa wajen kwanciya da gefe daya.

Michelle Cottle ta haifi jaririnta Orla ba rai a mako na 37 a shekarar 2016, bayan da ta yi goyon cikinta lafiya ba tare da wata alama da take nuna cewa akwai matsala ba.

Ta yi wani rubutu a shafinta mai suna “Dear Orla” inda kuma ta ji ra’ayoyi daga wurin matan da suka shiga irin wannan yanayin.

Michelle ta sake haihuwar wata ‘yar mai suna Esme bayan shekara daya, ta ce yana da muhimmanci iyaye su dinga aiki da irin wannan shawara da ake bayarwa don gujewa afkuwar abun da ba shi kenan ba.

“Ina ganin hakan zai taimakawa mutane, wajen gujewa abu mara kyau da ka iya faruwa, da kuma samun kyakkyawan yanayi fiye da na mutanen da suke samun matsala.

kuma bugu da qari yaka mata kusani cewa

“Ko wanne lokaci ana iya samun wani yanayi da ba kasan ko jaririnka yana da rai ko babu ba, wannan wani abu ne na tashin hankali,” in ji ta.

“Da daddare ne abun ya fi muni saboda mutane da dama suna iya cewa sun yi amanna cewar wata kila jariransu suna mutuwa ne a lokacin da suke bacci. Ina ganin wannan zai iya haifar da tsoro saboda yin bacci dai dole ne.”

“Saboda haka ina ganin abubuwa a bayyane da za su iya taimaka maka abu ne mai mai matukar muhimmanci ga mata.”

allah ya sa mudace duniya da lahira amin ya Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button
WP2Social Auto Publish Powered By : XYZScripts.com